OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutune Tara A Mabanbantan Hare-hare A Kaduna

'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutune Tara A Mabanbantan Hare-hare

 

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce ‘yan bindiga sun kashe mutane tara da jikkata wasu guda biyu a mabanbantan hare-hare da suka kai kananan Hukumomin Chikun da Zaria da Zangon Kataf.

Sanarwar da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar a yau Juma’a, gwamnatin ta ce an kashe mutum uku yayin da yan bindigar suka yi wa garuruwan Buruku da Udawa tsinke.

‘Yan bindigar sun kuma kashe mutum daya da raunata wani gudan yankin Yola da Kadi da ke karamar Hukumar Chikun.

Wasu mutum biyu ‘yan bindigar suka kashe a kauyen Sako da ke Zangon Kataf, an kuma gano gawarwakin mutum biyu a yankunan Kurfi da Magamiya da ke a Zangon Kataf din.

Haka ma a karamar Hukumar Zaria, an kashe mutum daya a kauye Saye.

Da yake bayyana bacin ran sa kan lamarin, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El Rufa’I ya taya wadanda suka rasa ‘yan uwan su alhinin rashin, da kuma fatan wadanda suka samu raunuka za su samu sauki cikin gaggawa

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci