OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Jam’iyyar APC a Kaduna ta musanta shirin dakatar da El-Rufai

Jam’iyyar APC a Kaduna ta musanta shirin dakatar da El-Ruf

Governor Nasir El Rufa'i of Kaduna

Jam’iyyar APC a Kaduna ta musanta ikirarin dakatar da tsohon gwamnan jihar Nasir el-Rufai dake yawo a kafofin sada zumunta.

 

Salisu Wusono, mai magana da yawun jam’iyyar APC ta Kaduna ne ya bayyana hakan ga jaridar TheCable a ranar Talata. 

 

Salisu yace "Babu batun dakatar da El rufa'i daga jamiyyar". 

 

Idan zaku iya tunawa rahotanni sun tabbatar da El-Rufai na iya fuskantar dakatarwa saboda zargin sa da yiwa jamiyyar zagon kasa.

 

Wasu rahotanni sun tabbatar da an gano El-Rufai tare da dakataccen Sanata Abdul Ningi a kwanakin baya an kuma hango El-Rufai ya ziyarci hedikwatar jam’iyyar SDP da ke Abuja.

 

Wadannan ziyarce-ziyarcen sun janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta, a daidai lokacin da ake ta yada jita-jitar cewa tsohon gwamnan na shirya daukar wani matakin siyasa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci