OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Hukumar Lafiya ta tabbatar da ba a samu bullar zazzabin Lassa ba a Kaduna

Hukumar Lafiya ta tabbatar da ba a samu bullar zazzabin Lass

Hukumar lafiya matakin farko ta jihar Kaduna, ta bayyana cewa jihar bata samu bullar cutar zazzabin Lassa ba a makonnin da suka gabata.

 

Ibrahim Hamza-Ikara, Daraktan Kiwon Lafiya yayin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na kasa a ranar Laraba a Kaduna, ya ce a halin yanzu babu bullar cutar zazzabin Lassa a jihar.

 

 Ya bayyana cewa an sallami dukkan wadanda ake zargin sun kamu da zazzabin lassa daga asibitoci.

 

 Ya kara da cewa, “ an sallami sauran mutane takwas da suka warke daga cutar. "

 

Hamza-Ikara ya ce jihar za ta ci gaba da gudanar da shirin wayar da kan jama’a kan yadda za su inganta tsaftar muhallin su.

 

Zazzabin Lassa wani nau'in zazzabi dake haifar da alamun zazzabi, ciwon kai da kasala.

 

 

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci