OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Wasikar El-Rufai ga Buhari: Shehu Sani Ya Zargi Gwamna Da Ta’azzara Rashin Tsaro A Kaduna

Tsohon Dan majalisar dattawa a jihar Kaduna kuma jigo a jam’iyyar PDP, Sanata Shehu Sani, ya zargi gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna da kara ta’azzara ta’addanci a jihar.

Sanatan ya yi wannan zargin ne a lokacin da yake mayar da martani ga wata takarda da gwamnan ya rubuta wa shugaban kasa Muhammadu Buhari a kwanakin baya, inda ya kara nuna fargabar cewa 'yan ta'addar Ansaru na kafa gwamnati a jihar.

Da yake magana a gidan talabijin na Arise a ranar Asabar, tsohon dan majalisar ya ce babu wani sabon abu a wasikar, inda ya kara da cewa gwamnan na kokarin wanke kansa ne kawai.

Mista Sani ya bayyana cewa an san batutuwan da ke cikin wasikar tsawon shekaru bakwai, duk da cewa gwamnan da mukarrabansa na musantawa.

 “Lokacin da nake Majalisar Dattawa, na ci gaba da gabatar da kudiri game da lamarin, amma Gwamna da ire-irensa sun bayyana ni a matsayin wanda ke zagon kasa ga ci gaban jihar tare da wuce gona da iri.” Inji shi.

“Babu wani abu na musamman game da wasikar da gwamnan ya rubutawa shugaban kasa.  Jihar Kaduna dai ta shafe shekaru da dama tana fama da hare-haren ‘yan bindiga.  

"A yanzu haka, ita ce cibiyar kungiyar ta’addanci da masu garkuwa da mutane.

 “Wasikar da gwamna El-Rufai ya aikewa shugaban kasa ita ma ta yarda cewa gwamnati ta gaza a kowane mataki saboda ta gaza wajen kare rayukan al’ummarta.

 “Hakika ‘yan ta’adda sun kafa gwamnatinsu, sun kafa tsari, suna nada shugabanni, suna karbar haraji, sun kafa kotu, sun sasanta rigingimu da kuma samar da tsaro ga mazauna kauyuka.

 "Wasikar gaskiya ce amma wanda ya rubuta wasikar kuma yana taimakawa wajen tabarbarewar tsaro saboda a shekarun da suka wuce, sun kaucewa fadawa shugaban kasa halin da jihar ke ciki," in ji Mista Sani.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa Shehu Sani ya kuma zargi gwamnan jihar da rashin yin abin da ya dace wajen tallafawa hukumomin tsaro a jihar.

 “Gwamnatin Kaduna ba ta taka rawar gani ba wajen magance matsalar rashin tsaro kuma babu ( isasshiyar goyon bayan) ga jami’an tsaro da ke aiki a jihar da wasu furucin sa (gwamnatin) ya sanya ‘yan ta’addan suka shiga Kaduna.

 “Gwamnan ba ya da himma wajen samar da tsaro ta fuskar tallafi, lamarin tsaro ba zai kai haka ba idan har gwamna da takwarorinsa na jihohin da abin ya shafa sun yi amfani da albarkatun da jihar su ke da su wajen taimakawa jami’an tsaro,” in ji Mista Sani.

Bugu da kari, tsohon dan majalisar ya kuma yi zargin cewa kananan hukumomi biyu ne kadai ke da tsaro a Kaduna – Kaduna ta Arewa da kuma Kaduna ta Kudu.

“Gwamnati ta gaza tsawon shekaru, kuma nasarar yaki da ta’addanci ba ta da yawa.

 Ya kara da cewa, "Babu wani aiki da ya samu nasarar ceto dimbin mutanen da ake garkuwa da su, ana barin iyaye da 'yan uwa su biya kudin fansa domin a sako 'yan uwansu."

Har yanzu dai mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye, bai mayar da martani kan wannan zargi ba, saboda ba a amsa sakonnin da aka aike zuwa lambar wayarsa ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci