OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Tsohon Sakataren Gwamnatin Katsina Ya Sauya Sheƙa Zuwa PDP

Tsohon Sakataren Gwamnatin Katsina Ya Sauya Sheƙa Zuwa PDP

Tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Inuwa ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar PDP mai adawa.

Mista Inuwa a baya bayannan ya sha kaye a yunƙurinsa na neman tikitin takarar gwamna a jam’iyyar APC.

Yayin da ya shaida wa magoya bayansa a ranar Lahadi a Katsina cewa, matakin ya biyo bayan tattaunawa da magoya bayansa da sauran masu ruwa da tsaki a faɗin jihar.

“Idan za a iya tunawa, a lokacin zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar APC a jihar, mun san duk abin da ya faru a wancan lokacin, kuma a ƙarshe an bayyana wanda ya yi nasara.

“Mun amince da shan kaye kuma mun yi alƙawarin marawa dan takarar jam’iyyar baya, bayan da ya ziyarce ni kuma na ba shi tabbacin goyon bayan da ya dace.

“Amma abin takaici, tun a wancan lokacin, ba a taɓa tuntuɓa na da wani aiki da ya shafi ci gaban jam’iyyar a jihar Katsina ba.

“Wannan alama ce ƙarara cewa ba a mutunta mu a matsayin ƴan jam'iya ba yayin da wasu ke cewa za su iya cin zaɓe ko da ba mu.

“Da wannan abun da ke faruwa a jam’iyyar, ba za mu iya ci gaba a cikin wannan hali ba, don haka ni kaina da dukkan magoya bayana mun yanke shawarar barin jam’iyyar tare da marawa PDP baya,” inji shi.

Inuwa ya umurci dukkan magoya bayansa a faɗin jihar da su yi rajista da PDP tare da mika ofisoshin yaƙin neman zaɓensa ga jam’iyyar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci