OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Tinubu Ya Min Tayin Tikitin Sanata A APC, Cewar Wike

Tinubu Ya Min Tayin Tikitin Sanata A APC, Cewar Wike

Gov. Nyesom Wike

Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike ya ce ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, yayi masa tayin takarar kujerar Sanata.

Daily Trust ta ruwaito yadda Tinubu da Wike suka haɗu a Landan a watan da ya gabata a daidai lokacin da rikicin  jam’iyyar adawa ke ƙara ƙamari.

Bayan ganawar Wike da Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya garzaya kasar Birtaniya, inda ya sake ganawa da Wike.

Duk da haka haɗuwar Atiku da Wiken bai rage ko kwantar da hankulan jijiyar wuya ba yayin da Wike da abokansa suka nace cewa dole ne Sanata Iyioricha Ayu ya ajiye mukaminsa domin samun zaman lafiya.

Wike ya bayyana haka ne a yayin da yake mayar da martani a wani shirin talabijin kai tsaye a ranar Juma’a.

Wike ya ce, “Ban tsaya takara ba don in zama ɗan takarar mataimakin shugaban kasa, ni ba kamar sauran da ba su da kima suka sayi fom din Sanata tare da fom din shugaban kasa bane.

"Shi ya sa lokacin da Tinubu ya baya ni tikitin sanata ban karɓa ba, Idan ina son mulki ko ina son in yi mulki, da na karɓi tikitin takarar.  

"Amma na ce a'a, Wannan shi ne mutumin da ya yi imani da adalci da gaskiya.

“Baya ga Tinubu, wanda ya fito daga APC, sauran jam’iyyun siyasa suna nema na har da Labour Party, saboda duk sun san kimata da kuma yadda zan iya tabbatar da cewa sun ci zabe a 2023. 

"Amma ban amince da ko ɗaya daga cikin tayin da wadancan bangarorin suka gabatar ba.”

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci