OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

2023: Tinubu Ba Zai Iya Siyan Kudu Maso Yamma ba – Tsagin Atiku

2023: Tinubu Ba Zai Iya Siyan Kudu Maso Yamma ba – Tsagin

Atiku, Tinubu

Tsagin Atiku Abubakar ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu ba zai iya saye ko kuma murde yankin kudu maso yamma ba bayan rahotannin kungiyar Afenifere sun amince da shi.

 Shugaban kungiyar ta Afenifere Pa Ayo Adebanjo ne ya karyata amincewar da aka ruwaito, kuma mai magana da yawun yakin neman zaben Atiku, Kola Ologbodiyan, ya bayyana cewa Tinubu ya zabi siyasar kabilanci ne domin kawar da hankalin jama’a daga rashin cancantarsa.

 “Ya kamata Tinubu ya sani cewa ba zai iya murdewa ko siyan Kudu maso Yamma ko wani yanki na kasar nan yadda ya siya tikitin takarar Shugaban kasa na APC ba; tikitin da aka kwatanta da dalar Zimbabwe"

"Ya kamata masu rike da mukamin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC su sani cewa yankin Kudu maso Yamma kamar sauran sassan kasar nan, sun daura alhakin tabarbarewar alamuran Kasarnan a cikin Shekaru balwai da rabi na gwamnatin APC a wuyan Tinubu domin shi ya shaida cewar Yana da hannu wajen daura wannan Gwamnati" in ji shi.

 Ziyarar da Tinubu ya kai wa daya daga cikin shugabannin kungiyar siyasa da zamantakewar kabilar Yarbawa, Pa Reuben Fasoranti ta janyo Cecekuce a tsakanin al'umma.

Yayin ganawar bangarorin biyu Fasoranti ya yi wa dan takarar shugaban kasa addu'a yayin Hadi da Sanya masa albarka.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci