OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Tinubu Ya Bada Tallafin Naira Miliyan 100 Ga Waɗanda Ambaliyar Ruwa Ya Ritsa Dasu a Kano

Tinubu Ya Bada Tallafin Naira Miliyan 100 Ga Waɗanda Ambali

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC mai mulki, Sanata Bola Ahmed Tinubu ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 100 ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Kano.

Tinubu ya kai ziyara Kano ne domin ƙaddamar Da ofishin yaƙin neman zaɓen Gwamna dana Shugaban ƙasa Na Jam’iyyar APC a Kano.

Ya sanar da bayar da tallafin ne a liyafar cin abincin dare da ƴan kasuwar Kano suka shirya domin karrama shi a daren Asabar.

Tinubu ya tabbatar wa ƴan kasuwar cewa buƙatar da suke da ita  na bunƙasa harkokin kasuwanci ba za a yi fatali da ita ba idan ya ci zaɓen shugaban ƙasa a 2023.

Ɗan takaran ya ce abun yana ba shi mamaki yayin da ƴan adawa ke ƙara jaddada cewa ba shi da lafiya.

''Nayi kama da marar lafiya?  Tinubu ya tambayi mahalarta taron.

''Ina da lafiya sosai kuma lafiyayye ne ni, Ba ina yin takara bane don kokawa ko yaƙi ba.

‘’Na tsaya takarar shugaban ƙasa ne wanda ake amfani da hikima kuma aiki ne na ilimi."

A nasa jawabin, gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce jam’iyyar APC tana lashe tikitin tsayawa takara saboda nasarorin da gwamnatin shugaban Buhari take samarwa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci