OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Sojoji Sun Bankado Sansanin Yan Ta'adda A Abuja

Sojoji Sun Bankado Sansanin Yan  Ta'adda A Abuja

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta bankado sansanin yan ta'adda a unguwar Deidei mayanka dake yankin Abuja Municipal da kuma kauyen Dukpa dake Gwagwalada a birnin tarayya Abuja.

A yayin sumamen rundunar sojin ta yi nasarar kama mutane takwas da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram ne hadi da kama wasu makamai da harsashi.

Darektan yada labarai na rundunar manjo janar Musa Danmadami ne ya bayyana hakan ga manema labarai a shelkwatar Rundunar dake birnin tarayya. Inda yace sun kama bindigu kirar AK-47 guda biyar, Kananan bindigu Uku, Adduna da wukake hadi da kulin tabar wiwi a sansanin yan ta'addan.

Biyo bayan karuwar hare- hare a yan kwanakin nan ya sanya ake zargin cewar mayakan kungiyar Boko Haram da ISWAP sun kafa sansaninsu a birnin tarayyar domin haddasa barna.

Hakan yasa a ranar 13 ga watan Augusta rundunar sojin tayi dirar mikiya a yankunan da ake zargin sun kafa sansanin nasu aka kumayi nasarar kama su kamar yadda manjo janar Danmadami ya bayyanawa jaridar Daily Trust.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci