OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Ahmad lawan ya gana da hukumomin tsaro kan zargin kisan wasu fararan hula a Yobe

Ahmad lawan ya gana da hukumomin tsaro kan zargin kisan wasu

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa kuma Sanata mai wakiltar Yobe ta Arewa, Ahmad Lawan ya gana da shugabannin hukumomin tsaro kan zargin kashe fararen hula da sojoji suka yi a jihar. 

 

Taron wanda ya gudana a ranar Lahadi a gidansa da ke Gashua, ya nemi lalubo hanyoyin dakile afkuwar wannan mummunan lamari a nan gaba.

 

 Allnews.ng ta rawaito cewa sojoji sun kashe wasu fararen hula uku a ranar 14 ga Afrilu, 2024 wadanda suka yi zanga-zangar nuna rashin Jin dadin su kan kisan buge wani matukin babur mai kafa uku da wata motar sintiri ta sojoji ta yi.

 

Lawan wanda a halin yanzu yake shugabantar kwamitin tsaro na majalisar dattawa ya bukaci sojojin Najeriya da su binciki lamarin.

 

A karshen makon da ya gabata ne Sanatan ya ziyarci wadanda suka samu raunuka a asibiti ya kuma umarci gidauniyarsa ta Sanata Ahmad Ibrahim Lawan (SAIL) Foundation ta biya dukkan kudin asibitinsu dana magani. 

 

A yayin ganawarsa da shugabannin tsaro, Sanatan ya nuna matukar damuwarsa kan lamarin tare da jaddada bukatar sojoji su bi ka’idojin aiki tare da mutunta hakkin dan Adam.

 

 Ya kuma jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da al’ummar yankin wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiyar al’ummar Yobe ta Arewa. 

 

Sanatan wanda ya bayar da cikakken bayanin taron a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ya ce shugabannin tsaro sun yi masa bayani kan matsalar tsaro a mazabarsa, ya kuma ba da tabbacin za su yi bincike sosai kan lamarin tare da daukar matakin da ya dace a kan wadanda suka aikata laifin.

 

"Na bukaci jami'an tsaro da su kasance masu gaskiya a binciken da suke yi, su kuma hukunta masu laifin a kan abin da suka aikata. Na kuma yi kira da a kara himma wajen ganin an magance musabbabin tashe tashen hankula a Yobe ta Arewa da kuma samar da tattaunawa da sulhu a tsakanin masu ruwa da tsaki." Acewar sa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci