OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

Wata kungiya ta gudanar da taron addua a ranar tunawa da mariya Umaru Musa Yaradua

Wata kungiya ta gudanar da taron addua a ranar tunawa da  ma

Wata kungiya mai zaman kanta mai suna Pleasant Library and Book Club a jihar Katsina ta gudanar da addu’o’i na musamman a masallatan Juma’a domin tunawa da marigayi shugaba Umaru ‘Yar’aduwa.

 

Dr. Mukhtar Alqasim, daya daga cikin yayan kungiyar ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Katsina a ranar Juma’a, yayin bikin tunawa da ‘Yar’Adua karo na 14 wanda ya rasu a ranar 5 ga watan Mayun 2010.

 

Alqasim ya bayyana cewa PLBC ta kai ziyara ga limamai a fadin jihar, inda suka bukaci a shigar da addu’ar a cikin hudubarsu ta Juma’a, wadda aka gudanar da ita yadda ya kamata. 

 

Hakazalika, a wani bangare na tunawa da marigayin sun shirya ziyarar gidajen marayu, gidajen tsofaffi, wuraren kula da masu tabin hankali, da sauran wurare.

 

Alkassim yace " muna da tsare-tsare a lokacin ziyarar ranar Asabar, don raba kayan abinci, tufafi da sauran abubuwan da ake bukata zuwa waɗancan gidaje da cibiyoyin"

 

A ranar Lahadi, PLBC za ta kaddamar da wani littafi mai shafuka sama da 300 mai suna: ‘Abin da Yar’adua ya koyar da ni" wanda ya kunshi darussa na tsawon shekaru 23 na rayuwa karkashin jagorancin marigayi shugaban kasar.

 

Shugaban PLBC Dr Muttaqa Rabe-Darma ne ya rubuta littafin kuma za a gabatar da shi yayin bikin. 

 

Hukumar PLBC ce ta shirya shirin, tare da cikakken goyon bayan gwamnatin jihar.’’ Alqasim ya ce a yayin taron a ranar Lahadi, wasu fitattun mutane za su yi magana kan marigayi shugaban, sannan kuma za a yi wani taron addu’a a wurin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci