OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Sojoji goma sun mutu a wani hatsarin jirgi a Kenya

Sojoji goma sun mutu a wani hatsarin jirgi a Kenya

Kenya Military Chief, Gen. Francis Ogolla

An sanar da mutuwar babban hafsan sojin kasar Kenya Janar Francis Ogolla da wasu jami'an sojoji 9 bayan wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu. 

 

Shugaban kasar Kenya William Ruto ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Alhamis. Daga bisani ya sanar da zaman makoki na kwanaki uku a fadin kasar.

 

Rahoton ya tabbatar da cewa hatsarin ya afku ne a yammacin kasar a gundumar Elgeyo Marakwet, jim kadan da tashin jirgin daga kauyen Chesegon. 

 

Babban Hafsan sojin da tawagar sa suna rangadi ne Inda suka ziyarci sojojin dake aiki a yankin 

 

Har kawo lokacin kammala wannan rahoton ba a san musabbabin hatsarin ba amman mutum biyu daga cikin mutane 12 da ke cikin jirgin sun tsira da rayukansu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci