OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Gwamnan Borno ya amince da bawa daliban jinya tallafin karatun miliyan 600

Gwamnan Borno ya amince da bawa daliban jinya tallafin karat

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya amince da sakin sama da Naira miliyan 600 na tallafin karatu ga daliban aikin jinya a kwalejin koyon aikin jinya ta jihar. 

Sakataren zartarwa na hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Borno, Malam Bala Isa ne ya bayyana amincewar gwamnan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa an ware N637,563,000 don biyan alawus alawus da rajistar daliban.

Isa ya bayyana cewa gwamnan ya amince da kudi naira miliyan 393,680 domin biyan alawus alawus na naira 30,000 ga dalibai 1,088 daga watan Janairu zuwa Disamba 2024. 

Da kuma Naira miliyan 41,383 domin bawa sabbin dalibai 997 da suka samu gurbin karatu tallafin karatu.

Ya kara da cewa gwamnan ya kuma amince da daukar fitattun dalibai hudu daga kowane bangare na kwalejin aiki kai tsaye.

Ya yi nuni da cewa Gwamna Zulum ya bukaci daliban da suka amfana da su yi karatun da nutsuwa tare da bayar da gudunmuwarsu ga ci gaban jihar.

Sakataren zartarwa ya kuma yabawa gwamnan bisa ba da fifikon da yake bawa bangaren ilimi.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci