OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Gwamnatin Tarayya zata samar da wuta a kananan hukumomi takwas a Sokoto

Gwamnatin Tarayya zata samar da wuta a kananan hukumomi takw

Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin maido da wutar lantarki a kananan hukumomi takwas na jihar Sokoto, bayan shafe kimanin shekaru goma babu wutar lantarki. 

Adelabu Adebayo, Ministan Wutar Lantarki ne ya bayyana hakan a lokacin da gwamnan jihar Ahmed Aliyu ya bayyana hakan a wata ziyarar aiki da ya kai ofishin sa.

Bayan alkawarin da ministan ya yi, an aike da wata tawaga daga ma’aikatar wutar lantarki domin tantance wuraren da abin ya shafa don dawo da wutar lantarki.

Mustafa Baba Umarah, Daraktan rarraba wutar lantarki a ma’aikatar wutar lantarki ta tarayya, ya magantu a lokacin tantancewar a karshen mako a Sakkwato. 

Ya bayyana cewa, tawagar gwamnatin tarayya za ta yi nazari sosai kan irin matsalolin da ke haifar da yanke wutar lantarki a cikin al’ummomin da abin ya shafa tare da bayar da rahoton daukar matakin da ya dace. 

Ya ba da tabbacin gwamnati ta himmatu wajen ganin dukkan ‘yan Najeriya sun samu wutar lantarki, ba tare da la’akari da inda suke ba.

Kwamishinan Makamashi na jihar, Sanusi Dan Fulani, Ya bayyana cewa, “Kananan hukumomi takwas da aka ware domin sake hadewa da cibiyar sadar da wuta ta kasa sun hada da; Isa, Sabon Birni, Goronyo, Wurno, Rabah, Gada, Illela da Gwadabawa.”

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci