OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Wani dan Najeriya yana kokarin kafa tarihi na shafe awowi mafi yawan yana karatun littafi

Wani dan Najeriya yana kokarin kafa tarihi na shafe awowi ma

Ajao Samson, tsohon shugaban kungiyar dalibai na kwalejin fasaha ta jihar Osun, na kokarin kafa sabon kundin tarihi na Guinness World Record. 

A cewar Ajao, yana kokarin kafa tarihin karatu mafi tsawo na sa’o’i 214 ba tare da ya tsaya ba.

Tun da farko a shafinsa na Facebook ya bayyana shirinsa na gudanar da karatun na sa’o’i 214. 

An fara karatun ne a dakin taro na Adolak da ke Osogbo a ranar Litinin, 6 ga watan Mayu, kuma ana sa ran za a kai har zuwa ranar Talata 14 ga watan Mayu 14, 2024. 

Kamar yadda ya sanar a shafinsa na Facebook ya fara karatun ne da karfe 11 na safiyar ranar Litinin.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ya riga ya zarce sa’o’i hudu ya shiga na biyar yana karatun.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci