OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Rundunar sojin Nijar sun kama kasurgumin dan bindiga Kachallah Mai Daji

Rundunar sojin Nijar sun kama kasurgumin dan bindiga Kachall

Rundunar sojin kasar Nijar ta cafke wani kasurgumin dan fashin dajin nan da aka fi sani da Kachallah Mai Daji kusa da garin Illela da ke kan iyaka a Jamhuriyar Nijar.

A cewar wani masani kan yaki da ta’addanci Zagazola Makama, Kachallah Mai Daji ya shafe sama da shekaru goma yana aikata ta’addanci da barna a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Makama ya ce, “Ya kashe mutane da dama, ya kona kauyuka, ya yi garkuwa da daruruwan mutane, sannan ya sanya haraji a kauyuka kusan shekaru goma.” 

A cewar rahoton, shugaban ‘yan fashin ya yi ta’adi musamman a yankin Illela, inda ya addabi kauyuka kamar Tozai, Sabon Garin. Darna, Darna Tsolawo, Tudun Gudali, Basanta, Dan Kadu, Takalmawa, Gidan Hamma, Ambarura, Gidan Bulutu, da dai sauran su a kewayen. 

Sojojin Nijar sun kama Kachallah Mai Daji a lokacin da yake yunkurin satar dabbobi a kan iyakar Najeriya da Nijar. 

Rahoton ya kara da cewa, "Dakarun kasar Nijar ne suka kama shi a lokacin da ya yi kokarin yin awon gaba da dabbobi ta kan iyakar kasar."

A ranar Lahadin da ta gabata, akalla mutane 11 ne aka ruwaito sun mutu yayin da biyar suka samu raunuka bayan da wasu motoci biyu suka bi takan wasu nakiyoyin da ake zargin 'yan bindiga ne suka binne a Gamboru-Ngala.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci