OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Sarki Charles III yayi bikin cika Shekara daya akan karagar mulkin Burtaniya

Sarki Charles III yayi bikin cika Shekara daya akan karagar

A ranar Litinin ne Sarki Charles III na Biritaniya ya yi bikin cika shekara daya da hawa karagar mulki.

Wannan na zuwa bayan an gano sarkin yana fama cutar kansa.

Bisa alada a irin wannan biki akan yi ta harbe-harbe da bindigogi a tsakiyar birnin Landan da kuma wasu wurare a fadin kasar Birtaniya amman a wannan karon ba a shirya wani taron a hukumance.

ƙasa da mako guda bayan Sarki Charles ya ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati tun bayan kamuwa da cutar Kansas.

Sarkin mai shekaru 75, wanda bai bayyana nau'in cutar kansar da ke dauke da shi ba, yace zaiso ayi dan kwaryakwaryan bikin wannan rana bisa la'akari da alakar hawansa da rasuwar mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth ta biyu.

Archbishop na Canterbury, Justin Welby wanda ya nada Sarki Charles shekara guda da ta gabata a Westminster Abbey ya yaba da "dattakon sarkin".

Bikin na zuwa ne a yayin da wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta Ipsos Daily Mail ta ga darajar shaharar Sarki Charles ta dan karu zuwa kashi 56. Ɗansa kuma magaji Yarima William da matarsa Catherine, Gimbiyar Wales, sun kasance mafi shaharar membobin gidan sarauta da kashi 69 cikin ɗari kowanne tun watan Afrilun da ya gabata.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci