OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

Gwamnatin Tarayya zata dauki mataki akan masu amfanin da shaidar karatun bogi

Gwamnatin Tarayya zata dauki mataki akan masu amfanin da sha

Gwamnatin tarayya ta gargadi ‘yan Najeriya da ke amfani da shaidar kammala karatu na bogi domin samun aikin yi. 

 

Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya sanar da wani sabon yunkurin zakulo tare da fallasa mutanen da suka samu mukamai ta hanyar damfara. 

 

Idan dai ba a manta ba gwamnati ta kafa wani kwamiti da zai binciki ayyukan jami’o’i masu zaman kansu sama da 100 da kuma wasu jami’o’in kasashen waje a jamhuriyar Benin da Togo da wasu kasashe bayan wani rahoton bincike da aka buga a jaridar Daily Nigerian.

 

Da yake jawabi a ranar Juma’a, Farfesa Mamman ya jaddada bazasu lamunci duk Wani yunkuri na ruguza tsarin ilima a kasarnan ba.

 

Farfesa mamman yace "Abin takaici ne a ce wanda ya kamata ya fita daga jamiar Najeriya da sakamakon jarabawa mai daraja ta 2:1 ko 2:2 a yanzu yana gabatar da takardar shaidar kammala karatun digiri mai daraja na farko na bogi"

 

Ministan ya bayyana akwai wani rahoto da kwamitin ma'aikatu ya hada kan yadda ake gudanar da bincike kan yawaitar cibiyoyi da ke ba da takardar shaidar karatun bogi.

 

Wannan rahoto, a cewar Mamman, za a yi amfani da shi ne don jagorantar murkushe matsalar.

 

Ba a san takamaiman matakan da za a dauka ba sai dai Ministan ya yi nuni da cewa akwai yuwuwar yin hadin gwiwa da hukumomin da abin ya shafa don tantance sahihancin bayanai da gano masu laifi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci