OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Shugaban majalisar Edo ya dakatar da yan majalisa uku dake goyan bayan mataimakin gwamnan da aka tsige

Shugaban majalisar Edo ya dakatar da yan majalisa uku dake g

A ranar Litinin ne kakakin majalisar dokokin jihar Edo, Blessing Agbebaku ya dakatar da wasu ‘yan majalisa uku bisa zargin yunkurin tsige shi da wasu manyan jami’an majalisar.

Daya daga cikin ‘yan majalisar da aka dakatar, Donald Okogbe, PDP, Akoko-Edo II, na goyon bayan mataimakin gwamnan da aka tsige, Philip Shaibu, kuma shi ne dan majalisa daya tilo da bai sanya hannu kan takardar tsige Shaibu ba.

Sauran biyun su ne, Adheh Emankhu Isibor, APC, Esan North-East I, da Iyamu Bright, PDP, Orhionnwon II.

Agbebaku ya kuma zargi mutanen uku da kawo bokaye suyi kulunboto a zauren majalisar a ranar 1 ga Mayu da misalin karfe daya na dare.

 Agbebaku ya ce an dakatar da ‘yan majalisar uku ne har zuwa wani lokaci, yana mai zargin cewa wasu yan ziga ne suka yi tasiri a kan su domin su kawo rudani tare da yin amfani dasu su tsige shugabannin majalisar.

Dakatar da ‘yan majalisar, ya haifar da rudani a majalisar yayin da ‘yan majalisar da abin ya shafa suka yi fatali da matakin dakatar da su. 

A wani zama da aka yi ta cece-kuce, an ga ‘yan majalisar uku da aka dakatar suna tada jijiyoyin wuya inda sukace “Mai girma Shugaban Majalisa, ba ka da hurumin dakatar da duk wani dan majalisa baki daya dole ne a fara kada kuri'a tukunna"

Daga nan sai shugaban majalisar ya dage zaman majalisar baki daya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci