OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

Gwamnatin tarayya ta samar da fara amfani da sabon jadawalin mafi karancin albashi daga yau

Gwamnatin tarayya ta samar da fara amfani da sabon jadawalin

Gwamnatin tarayya ta sanar da za'a fara amfani da sabon jadawalin mafi karancin albashi daga yau 1 ga watan Mayu.

 

Wannan na zuwa duk da kwamitin tattauna kan sabon jadawalin mafi karancin albashin Basu kammala tattauna ba.

 

Nkeiruka Onyejeocha, karamar ministan ma'aikata ce ta bayyana hakan yayin bikin ranar ma'aikata a Abuja.

 

Tace duk da taso kwamitin ya karkare tattaunawarsa a yau za ayi dukkan mai yiwuwa wajen ganin an samar da rahoton kunshin bayanai akan sabon mafi karancin albashin nan bada dadewa ba.

 

 Kungiyoyin na NLC da TUC sun dade suna Kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta kammala yin duba akan jadawalin mafi karancin albashin.

 

Inda a kwanakin baya suka bukaci gwamnatin ta biya dubu 615,000 a matsayin mafi karancin albashi domin bawa ma'aikata damar tafiyar da rayuwarsu daidai da halin tattalin arzikin kasa.

 

 Yan kwadagon since wasu gwamnonin sun Gaza biyan dubu talatin din da ake biyan ma'aikata a matsayin mafi karancin albashi, Wanda tsaurin yazo karshe a watan Afrilu bayan shekaru biyar ana amfani da shi.

 

Kamata yayi a dinga yin duba akan jadawalin mafi karancin albashin duk bayan shekaru biyar don tabbatar da anyiwa ma'aikata adalci.

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci