OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Bayan shekaru 10 rundunar soji ta kubutar yar Chibok da akayi garkuwa da ita

Bayan shekaru 10  rundunar soji ta kubutar yar Chibok da aka

Dakarun ‘Operation Desert Sanity III’ da ke karkashin Operation Hadin Kai (OPHK) dake aikin a Arewa maso Gabashin kasar nan a ranar Laraba, sun ceto wata ‘yar makarantar chibok da aka yi garkuwa da su, shekaru goma da suka shude.

 

Sojojin bataliya ta 82 dake karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno sun ceto Lydia Simon tare da ‘ya’yanta uku a ranar Laraba, 17 ga Afrilu, 2024. 

 

Shekaru 10 kenan da sace ta da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi tare da sauran ‘yan mata sama da 200 daga makarantar Sakandaren Gwamnati da ke garin Chibok a Jihar Borno a ranar 14 ga Afrilu, 2014. 

 

Zagazola Makama, mai sharhi kan alamuran tsaro a yankin tafkin Chadi, ya bayyana cewa Lydia, wacce aka yiwa lakabi da lamba 68 a cikin ‘yan matan makarantar da aka sace, ta tsere daga sansanin Ali Ngulde a tsaunin Mandara inda aka tsare ta tsawon shekaru da dama. Ta mika wuya ga dakarun bataliya ta 82 dake Ngoshe a karamar hukumar Gwoza ta jihar. 

 

Lydia tana dauke da ciki wata biyar kuma ta yi ikirarin cewa ita yar asalin garin Pemi ce da ke karamar hukumar Chibok.

 

A ranar 14 ga Afrilu, 2024 ne ake cika shekaru 10 da sace 'yan mata 276 da mayakan Boko Haram suka yi a makarantar sakandiren gwamnati ta garin Chibok a jihar Borno.

 

Da fari yan mata 57 daga ciki sun kubuta daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su kwanaki kadan bayan sace su, daga baya kuma an kubutar da 16, yayin da aka sako 107 a lokuta daban-daban ta hanyar tattaunawa tsakanin gwamnati da yan ta'addan.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci