OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

Kungiyar likitoci ta kasa ta koka bisa hauhawar farashin magunguna

Kungiyar likitoci ta kasa ta koka bisa hauhawar farashin mag

Kungiyar likitocin ta koka da tsadar magani a kasar nan, tace hakan yana dakile kiwon lafiya don Alumma basa iya biyan kudin asibiti dana magani.

 

Dr Uche Ojimah Shugaban kungiyar NMA na kasa ne yayi wannan koke yayin wani taron karawa juna sani a ranar Talata.

 

An gudanar da taron domin yin jan hankalin game da hauhawar farashin magunguna da sauran kayan aikin kula da lafiya a kasarnan.

 

Dr Ojinmah yace karin kudin maganin na dada ta'azzara talauci a tsakanin Alumma.

 

A watan fabrairun daya gabata ministan lafiyar farfesa Muhammad Pate ya sanar da cewar gwamnatin Tarayya zata yi dokar da zata kawo karshen wannan matsala saidai har yanzu abun yaci tura hakan yasa Alumma suka fara zargin akwai bukatar sake duba akan lamarin.

 

Shugaban kungiyar NMA yace "Yan Najeriya na tsunduma talauci sanadiyar biyan kudin kiwon lafiya ya kamata gwamnatin tarayya ta samar da bankin tallafawa bangaren lafiya domin bunkasa fannin"

 

"Idan har bamu kawo karshen wariyar da Ake nuna wa wajen kula da lafiyar Alumma, na mai kudi saban na talaka daban to bazai haifar da da mai Ido ba " acewar Dr Ojinmah 

 

Yayi kira da gwamnatin ta samar da tsare tsare kawar da matsalar hadi da kara adadin abubuwan da inshorar lafiya zata iya biyawa yan kasar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci