OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Sanatocin APC 22 Na Shirin Sauya Sheka Zuwa PDP— Femi Fani Kayode

Sanatocin APC 22 Na Shirin Sauya Sheka Zuwa PDP— Femi Fani

Tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma jigo a jam’iyyar APC, Femi Fani-Kayode.

Tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma jigo a jam’iyyar APC, Femi Fani-Kayode ya sanar da shirin Sanatoci 22 na jam’iyyar dake shirin sauya sheka zuwa PDP.

Ya bayyana cewa sunatocin na shirin sauya shekar ne saboda jam’iyyar ta hana su tikitin takara a zaben shekara ta 2023.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twittera Larabar da ta gabata, Kayode ya ce dole a yi wani abu don hana kara faruwar hakan.

“Sanatocin APC 22 suna barazanar sauya sheka zuwa PDP saboda an hana su tikitin komawa majalisar dattawa. Wannan yana da mahimmanci kuma dole ne a yi wani abu don hana su. Mutane da yawa sun damu sosai kuma mun roki shugaban da sakataren jam’iyyar APC na kasa da su sami sanatoci don hana su, saboda mu baza iya hakurin rasa su ba”. Inji Fani kayode

A safiyar yau ne jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda wasu Sanatoci bakwai suka fice daga APC zuwa wasu jam’iyyun adawa.

Mambobin Majalisar Dattawan da suka fice daga APC sun hada da Ibrahim Shekarau (Kano), Yahaya Abdullahi (Kebbi) Adamu Aliero (Kebbi), Dauda Jika (Bauchi), Ahmad Babba Kaita (Katsina), Lawal Yahaya Gumau (Bauchi), da Francis Alimikhena. (Edo).

Da yake zantawa da manema labarai bayan ganawar sirri da Sanatocin APC, Shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Adamu, ya ce baya jin dadin yadda ‘ya’yan jami’iyyar ke ta sauya sheka zuwa jam’iyyun adawa, musamman ganin yadda kakar zabe ke kara karatowa.

.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci