OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Jamiyyar PDP ta bada tabbacin gudanar da sahihin zaben fidda gwani a Jihar Ondo

Jamiyyar PDP ta bada tabbacin gudanar da sahihin zaben fidda

Mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Lawrence Ewhrudjakpo ya bada tabbacin gudanar da sahihin zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP a jihar Ondo bisa gaskiya da amana.

 

A yanzu haka ana gudanar da zaben fidda gwani na babbar jam'iyyar adawar a Akure, babban birnin jihar.

 

 Ewhrudjakpo, wanda shi ne shugaban kwamitin zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP na Ondo, ya ce "Muna jihar Ondo ne domin gudanar da zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar PDP, inda muke da ‘yan takara bakwai. Hukumar zabe ta amince da salon zabe uku yayin fidda gwani a cikin dokar zabe ta 2022, amma a yau, mun zabi mu gudanar da tsarin kato bayan kato"

 

 “Muna sa ran wakilai kusan 627 ne za suyi zaben kuma duk mun shirya, dukkan mambobin kwamitin suna nan, kuma an fara tantancewa. Don haka mun shirya kuma ’yan takarar suna cikin farin ciki sun tabbatar min cewa za su amince su yi aiki tare domin duk wanda ya fito takara, domin burin jam’iyyar mu ita ce yadda za a dawo da mulki daga hannun APC"

 

“Kuna sane ni ne na gudanar da zaben fidda gwani a jihar Osun kuma muka yi nasara a Osun. Na zo nan ne don gudanar da Jihar Ondo kuma da yardar Allah".

 

 Ya ce akalla ‘yan takara bakwai ne ke fafatukar zama dan takarar jam’iyyar a zaben gwamna da ke tafe a watan Nuwamba a wannan shekara.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci