OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Sama da mutum 170,000 ne za su kada kuri'a a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a jihar Ondo

Sama da mutum 170,000 ne za su kada kuri'a a zaben fidda gwa

Kwamitin da ke sa ido a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a jihar Ondo ya sanar da cewa mambobin jam’iyyar 171,922 ne kuri'a a zaben da za'a gudanar a ranar Asabar.

 

 Za a gudanar da zaben fidda gwanin ne a unguwanni 203 a kananan hukumomi 18, da masu neman takara 16, ciki har da gwamna mai ci Lucky Aiyedatiwa a cikin fafatawar.

 

Bayan wata ganawa da masu ruwa da tsaki da masu neman tsayawa takara a birnin Akure, sakataren kwamitin Sanata Ovie Omo-Agege, ya tabbatar da cewa babu daya daga cikin masu neman tsayawa takarar da ya janye takararasa.

 

Kwamitin ta tabbatar da zata gudanar da zaben fidda kwanin a daukacin unguwanni 203, tare da jaddada bukatar gudanar da shi cikin zaman lafiya tare da yin kira ga masu son tsayawa takara da su shawarci magoya bayansu su guji tada tarzoma yayin zaben. 

 

Omo-Agege ya yi alkawarin tabbatar da gudanar da sahihin zabe, cikin gaskiya da amana.

 

Hakazalika, ya ba da tabbacin hadin gwiwa da hukumomin tsaro na jihar domin tabbatar da doka da oda a duk lokacin da ake gudanar da zaben fidda gwanin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci