OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Manyan gidajen gyaran hali 3 da Buhari ya gina za su dauki fursunoni 9,000 – Aregbesola

Manyan gidajen gyaran hali 3 da Buhari ya gina za su dauki f

Fursunoni 9,000 ne za a iya ajiye wa a gidan gyaran hali guda uku da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ke ginawa, in ji ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola.

Ya ce cibiyoyi uku da aka gina a Karshi, Janguza da Bori sun kasance a matakai daban-daban na kammala su.

A cewarsa, gidajen uku suna daga cikin gidaje gyaran hali shida da shugaban ya amince a gina.

Ministan ya bayyana hakan ne lokacin da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ke zantawa da shi a Abuja, ya ce kankararrun ginin zamanin an rabasu ne zuwa shiyoyi shida na Najeriya.

Ya ce sabon aikin wani bangare ne na kudirin Gwamnatin Tarayya na yin garambawul gidajen gyaran hali a Najeriya.

“Gwamnatinmu a lokacin da ta karbi aiki ta yi shirin samar da kayan aiki na musamman wanda shida daga cikin irin wadannan wurare aka dade da fara aiki tun da farko.

“Abin burgewa game da wuraren da muke magana akai shine, yanzu muna da kayan aiki, muna kiran wurin Custodial Village facility, kowane daga gidan gyaran halin da ake ginawa zai iya ɗaukar fursunoni 3,000. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci