OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Farfesa Osinbajo Ya Jagoranci Taron Majalisar Zartarwa

Farfesa Osinbajo Ya Jagoranci Taron Majalisar Zartarwa

Mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranci taron mako-mako na majalisar zartarwa ta tarayya a yau Laraba a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya tafi ziyarar aiki ƙasar Portugal.

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha da shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa Farfesa Ibrahim Gambari suna daga cikin mahalarta taron.

Ministocin da suka halarci taron sun haɗa da na Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, sai na Shari’a, Abubakar Malami, Kasafin Kudi da Tsare-tsare na ƙasa, Zainab Ahmed.

Sauran sun haɗa da ƙwadago, Chris Ngige da Sadarwa da Tattalin Arziki na Digital, Dr Isa Pantami.

Sa'annan ministan Noma da Raya Karkara, Mohammad Abubakar, Muhalli, Mohammed Abdullahi da Lafiya, Osagie Ehanire.

Ƙaramin ministan kasafin kuɗi da tsare-tsare na ƙasa, Clem Agba da ƙaramin ministan lafiya, Adeleke Mamora suma sun halarci taron.

A taron da ya gabata a ranar 22 ga watan Yuni, majalisar ta amince da Naira biliyan 50 domin gyaran tituna a Taraba da Yobe da kuma gina tashoshin wuta don bunƙasa wutar lantarki a yankin Gwarinpa da ke babban birnin tarayya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci