OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Tsaron Iyakoki: Aregbesola Ya Yi Kiran Hadin Kai Da Al'umma

Tsaron Iyakoki: Aregbesola Ya Yi Kiran Hadin Kai Da Al'umma

Rauf Aregbesola

Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya yi kira da al'umma su sa hannu wajen sa ido kan iyakokin kasar.

Aregbesola ya ce shigar da shugabannin al’umma kan harkokin tsaron iyaka zai taimaka wajen karfafa tsaro a yankin.

Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke jawabi a taron Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Abuja.

Ya yi nuni da cewa al’ummomin da ke kan iyaka suna da alhaki na kishin kasa na dakile kwararar masu aikata laifuka cikin kasar tare da sauran hukumomin gwamnatin tarayya da ke da ruwa da tsaki a kan aikin. 

Yayin da yake mayar da martani game da haramtattun ayyukan da 'yan kasashen ketare ke ratsa kan iyakokin kasar, ya ce gwamnati na yin iyakacin kokarinta wajen ganin an tabbatar da hakan.

A cewar sa: “Muna kan haka, muna kara jan hankalin mutanen mu da su kasance a bakin iyaka yayin da muke inganta aikin sa ido a kan iyakokin da sauran su.

“Amma hakan ba zai wadatar ba, ina son ‘yan Najeriya su fahimci hakikanin cewa in dai a kan girman yanki ne, za mu kasance daya daga cikin manyan kasashe uku na farko a Afirka.

"Abin da hakan ke nufii shi ne, ba zai yiwu ku sami isassun ma'aikata waɗanda za su iya tsare kowane bangare na iyakokin ba."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci