OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Rikicin PDP: Gamayyar  Ƙungiyar Arewa Ta Ce Dole Ayu Ya Yi Murabus

Rikicin PDP: Gamayyar  Ƙungiyar Arewa Ta Ce Dole Ayu Ya Yi

Senator Iyorchia Ayu,

Gamayyar kungiyar matasan jam’iyyar PDP a Arewacin Najeriya, ta buƙaci shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu ya yi murabus.

Gamayyar ƙungiyoyin da suka gudanar da zanga-zanga a Sakatariyar PDP da ke Kaduna a ranar Juma’a, sun ce dole ne Ayu ya cika alƙawarin da ya ɗauka, ya yi murabus.

Wannan ya biyo bayan rikicin da jam’iyyar ta fuskanta tun bayan da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar domin zaben 2023.

Kakakin kungiyar, Shehu Isa-Dan’Inna, ya bayyana cewa PDP ba jam’iyyar Arewa ba ce, jam’iyya ce ta kowa da kowa, ko daga arewa ne ko kuma daga kudu, cewar Jaridar Punch.

“PDP ba jam’iyyar Arewa ba ce kuma ba jam’iyyar Kudu bace, dole ne mu kasance masu adalci da haɗin kai, domin samun nasara a matakai daban-daban a zaben 2023 mai zuwa.

"Idan rikicin cikin gida na PDP ya ci gaba, ba na tunanin za mu ci zaɓen shugaban kasa.

"Domin PDP ta fito da gaskiya kamar yadda ta saba yi, bai kamata Arewa ta rike mukamai kusan guda uku a jam'iyyar ba."

Isa-Dan’Inna, ya bayyana cewa wasu gwamnoni da shugabannin jam’iyyar PDP musamman daga kudancin Najeriya sun dage cewa, domin a yi gaskiya, bai kamata Arewacin Najeriya ya rike tikitin takarar shugaban ƙasa da na shugaban jam’iyyar ba.

"Yayin da yace ƴan ƙasar na buƙatar jam’iyyar PDP ta shugabance su don kawo sauyi a al'amuran da suka shafi rayuwar ƴan Najeriya baki ɗaya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci