OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

NiMet: Jihohin Gombe, Bauchi, Adamawa da Wasu Na Fuskantar Ambaliyar Ruwa

Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta sanya jihohin Gombe, Bauchi, Adamawa, Borno, Yobe, Katsina, Sokoto, jigawa, da kuma Kano cikin jerin sunayen jihohin da ke fuskantar barazanar ambaliyar ruwa.

Hukumar ta yi hasashen cewa za a iya fuskantar ambaliyar a watan Agusta, Satumba da Oktoba saboda yawan ruwan sama.

Shugaban hukumar Farfesa Mansur Matazu ne ya bayyana hakan a Abuja.

Matazu ya bayyana cewa jihohin Kebbi, Kaduna, Taraba, Nasarawa da Yobe na arewacin kasar za su fuskanci matsakaicin hatsarin ambaliya a cikin lokacin da aka bayyana.

Yayin da yake lissafta jihohin da za su fuskanci ruwan sama kamar yadda ya kamata a daidai wannan lokacin, ya bayyana jihohin Kudu-maso-Yamma kamar Osun, OYo, Ogun da Legas.

A cewar Matazu, wasu jihohin Kudu maso Gabas da Kudu-maso-Kudu za su fuskanci ruwan sama kamar yadda aka saba zuwa kasa da haka. 

Ya ce jihohin sun hada da: Bayelsa, Rivers, Akwa Ibom, Cross River, Abia, Imo, Anambra, Ebonyi da Enugu.

Shugaban ya kuma yi kira ga dukkan hukumomin bada agajin gaggawa da su kasance cikin shiri yayin da suke tsara shirye-shiryen wayar da kan al’umma.

Ya yi kira ga hukumomin da su “fara wayar da kan jama’a ta hanyar anfani da ma’aikatan da ke aiki a fili don yiwuwar ayyukan taimako musamman a wuraren da ke da hatsari,” kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci