OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gwamnatin jihar Adamawa ta biya bashin kudaden fensho

Gwamnatin jihar Adamawa ta biya bashin kudaden fensho

Gwamnatin jihar Adamawa ta ce kawo yanzu ta kashe Naira biliyan 5 wajen biyan maaikatan gwamnati da suka yi ritaya da ga cikin bashin Naira biliyan 20 da ake binta na kudaden fensho.

 

Ibrahim Attah, mamba na dindindin a hukumar ta fansho ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Yola ranar Litinin.

 

Ya ce an fitar da Naira biliyan 1.5 da kuma Naira biliyan 3.5 a kashi biyu da aka yi amfani da su wajen daidaita bashin da ake bi ga wadanda suka cancanta, yana mai jaddada cewa an biya dubban wadanda suka yi ritaya albashi.

 

Ya kara da cewa gwamnati ta na sakin Naira miliyan 50 duk wata ga hukumar domin ci gaba da biyan hakkokin wadanda suka yi ritaya.

 

Ya ce gwamnatin Ahmadu Fintiri ta jajirce kuma ta kuduri aniyar inganta rayuwar yan kasa musamman maaikata.

 

Ya kara da cewa "Gwamnati ta bayar da gudummawa sosai wajen samar da ababen more rayuwa, karfafawa matasa da kuma tsaro."

 

NAN

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci