OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Ni Da Goje Ba Mu Sani Ba Ko Za Mu Ga Shekarar 2023, Cewar Inuwa Yahaya

Ni Da Goje Ba Mu Sani Ba Ko Za Mu Ga Shekarar 2023, Cewar In

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce shi ko tsohon gwamnan jihar, Sanata Danjuma Goje ba su san ko za su ga 2023 ba.

Gwamnan ya yi wannan tsokaci ne a ranar Talata a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a fadar shugaban kasa da ke, Abuja.

A halin yanzu babu masaniya akan abin da ya shiga tsakanin jigajigan na jihar.

Sanata Danjuma Goje ya ziyarci Gombe ne domin daurin aure a ranar Juma’a inda wasu da ake zargin ‘yan daban siyasa ne suka kai wa motar sa hari.

A wata sanarwa da Lilian Nworie, mai taimaka wa Sanatan kan harkokin yada labarai ta fitar, ta ce 'yan daban siyasa ne masu biyayya ga Gwamna Yahaya.

Sanatan ya kai kara wurin babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF), Abubakar Malami inda ya bukaci a gudanar da bincike a kan lamarin yayin da ya sanar da sufeto Janar na ‘yan sanda, Alkali Baba; shugaban hukumar 'yan sanda, ministan harkokin 'yan sanda da kuma kwamishinan 'yan sanda na jihar Gombe.

Gwamnan wanda ya yi magana ranar Talata a Abuja ya ce alkawarin da ya yi shi ne kawo karshen ayyukan kungiyar Kalare a jihar.

Ya kuma yi kira ga mutanen da ke hulda da kungiyar da su daina.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa al’amuran tsaro sun lafa yayin da jama’a ke ci gaba da gudanar da harkokin yau da kullum.

Da yake amsa tambaya kan ko dalilin fadan nasu yana da alaka da neman sake tsayawa takara a zaben 2023, Yahaya ya ce, “To, abin da ya kamata ku sani shi ne Allah ne kadai ya san gobe. Ni da Goje ba mu san ko za mu ga shekarar 2023 ba."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci