OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Inuwa Yahaya zai gina tashar samar da wuta daga hasken rana mai karfin Megawatt 250

Inuwa Yahaya zai gina tashar samar da wuta daga hasken rana

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana shirin gina tashar samar da wutan lantarki daga hasken rana mai karfin Megawatt 250 a jihar.

Gwamnan ya ce aikin zai kasance tare da hadin gwiwar kamfanin samar da wutar lantarki na Neja Delta (NDPHC).

Yahaya ya bayyana haka ne a lokacin da yake bude taron zuba jari na farko na Gombe (GoInvest) a jiya a babban dakin taro dake jihar.

A cewar sa, wutar lantarkin mai karfin megawatt 250 shine aikin makamashi na biyu da gwamnatin sa ke zuba jari a ciki.

Ya kara da cewa, jihar a karkashin shirin kungiyar gwamnonin jihohin Arewa na kara saka hannun jari a kan karin Megawatt 100.

Da take jawabi a wajen taron, mai baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan sauwaka kasuwanci, Dr Jumoke Oduwole ta yaba wa gwamna Yahaya bisa jajircewa da basirar sa. 

Ku tuna cewa jihar Gombe ta samu suna a matsayin jiha ta daya a jerin masu saukaka harkar kasuwanci a Najeriya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci