OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Inuwa Yahaya Ya Taya Musulmai Murnar Maulidi, Yayi Kiran Zaman Lafiya

Inuwa Yahaya Ya Taya Musulmai Murnar Maulidi, Yayi Kiran Zam

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya taya al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar Maulidi ta 2022.

Gwamna Yahaya ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su ci gaba da daukar darasi da koyi daga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW).

A wata sanarwa da mai magana da yawun sa Ismaila Uba Misilli ya sanyawa hannu, Yahaya ya yi kira ga al’ummar musulmi da su yi koyi da juriya, tawali’u, kunya da gaskiya kamar yadda rayuwar Annabi Muhammad (SAW) ta nuna.

A cewar sa: "Yayin da muke bikin wannar babbar rana dake zagayowa sau ɗaya a duk shekara, ina ƙira a gare mu, mu ci gaba da ɗabbaƙa halaye da ɗabi'un da Ma'aikin Allah (SAW) ya koyar a harkokin rayuwar mu na yau da kullum".

Ya kara da cewa, "Yana da muhimmanci mu yi waiwaye ga koyarwar sa tare da ɗabbaƙa halayen sa na karfafa haɗin kai, nagarta, zaman lafiya da ƙauna ga ƴan uwa da maƙwabta, domin waɗannan ɗabi'un suna da matuƙar muhimmanci a ƙoƙarin mu na samun ci gaba mai ma'ana da tafiyar da jiha da ƙasar mu mai mabambantan al'ummomi".  

Sanarwar ta ci gaba da cewa, gwamnan ya ce: “Kamata yayi bikin maulidin na fiyayyen halitta ya kasance wata muhimmiyar dama ta sake kyautata alaƙa da mahaliccin mu dama ƙarfafa haɗin kan mu ta hanyar yin addu'o'in ci gaba da kwanciyar hankali ga Jihar mu ta Gombe da ƙasa baki ɗaya musamman a irin wannan lokaci da ƙasar nan ke fama da matsalolin tattalin arziƙi, da zamantakewa."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci