OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Mutum 8 Sun Tsira Daga Kifewar Kwale-Kwale A Kaduna

Mutum 8 Sun Tsira Daga Kifewar Kwale-Kwale A Kaduna

Boat Mishap

 Wani manomi ya nutse a ruwa inda wasu mutum takwas suka tsira a hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Kabala Doki jihar Kaduna.

Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:30 na safiyar ranar Lahadi inda wanda abin ya shafa, mai suna Umar, ya hau kwale-kwalen da niyar taimakawa mutanen da suka makale a dayan gabar kogin amma sai kwale-kwalen ya kife.

Wani mazaunin garin da ya bayyana sunansa da Murtala Kabala ya shaida wa Daily Trust cewa wanda ya nutsen sananne ne a wannan yankin kuma yana da gona a kusa da kogin.

“Mun damu kwarai sanin cewar Umar ya iya iyo kuma ya dade yana aikin noma a bakin kogin tsawon shekaru.

Wannan ne ya sa muka yi mamaki da muka sami labarin cewa ya nutse a cikin kogi a kokarin sa na ceto mutanen da suka makale a gefen kogin.

Allah ya jikan sa,” inji shi.

An sami labarin cewa shi kadai ne kawai ya nutse; sauran da ke cikin jirgin sun tsira.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban karamar hukumar Kaduna ta Arewa, Muktar Baloni, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya shaida wa Daily Trust cewa har yanzu ba a gano gawarsa ba.

Shugaban Ya koka da yadda wani bangare na karamar hukumar ke fama da ambaliyar ruwa, yana mai cewa suna kokarin tattara bayanai na gidajen da abin ya shafa domin taimakawa wadanda abin ya shafa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci