OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 50 A Adamawa

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 50 A Adamawa

A ƙalla Mutane 50 ne daga al’ummomi 11 a jihar Adamawa suka rasa rayukansu a ambaliyar da ta afku a kwanakin baya, yayin da wasu 71 suka samu raunuka.

Hakan na ƙunshe cikin wata Sanarwar da ta fito a ranar Juma’a ta hannun babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Adamawa (ADSEMA), Malam Suleiman Mohammed.

A yayin wata zantawa da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), Mohammed ya ɗora alhakin ambaliyar ruwa a kan sakin ruwa daga madatsar ruwan Lagdo da ke makwabciyar ƙasar Kamaru.

A cewarsa, bala’in ya yi sanadiyar lalata gonaki 172,000 da kayan abinci na miliyoyin naira.

“Wasu daga cikin ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Numan, Shelleng, Yola ta Kudu, Yola ta Arewa, Demsa, Mayo Belwa da Michika,” in ji shi.

Mista Mohammed ya bayyana cewa hukumar ta samar da tufafi da kayan abinci da magunguna da gidajen sauro da barguna da guga ga wadanda abin ya shafa domin rage musu radadi.

"Gwamnatin Jiha da ta Tarayya da sauran masu hannu da shuni ne suka bayar da kayayyakin.”

Da yake jawabi, ya ƙara da cewa hukumar za ta haɗa kai da hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa domin kai al’ummomin da abin ya shafa zuwa wurare masu tsaro.

"Za mu ci gaba da wayar da kan al'umma game da haɗarin da ke tattare da zama a yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci