OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ambaliyar Ruwa: Kwararrun Likitoci Sun Yi Gargadi Game Da Annobar Da Ke Tafe

Ambaliyar Ruwa: Kwararrun Likitoci Sun Yi Gargadi Game Da An

Kungiyar likitocin Najeriya (NMA) ta yi gargadin cewa kasar na cikin hadarin kamuwa da cututtuka saboda yawaitar cututtuka masu yaduwa a cikin ruwa a yayin da ake fama da ambaliyar ruwa a fadin kasar.

 A ranar Larabar da ta gabata ne shugaban NMA, Dr Uche Ojinmah, ya yi wannan gargadin, inda ya bukaci gwamnatin tarayya da ta tashi tsaye domin dakile matsalar.

 A cewarsa, ya kamata gwamnati ta samar da kyakkyawan sansani, bandaki, ruwa da kuma kiwon lafiya ga wadanda ke zaune a yankunan da ambaliyar ta fi shafa, musamman a wurare kamar Bayelsa da gawarwaki suka fara shawagi a cikin ruwa.

 Rijiyoyi da magudanan ruwa sun riga sun gurɓata don haka akwai haɗarin kamuwa da cututtuka na ruwa, musamman a jihohin da abin ya shafa.

"Gawawwaki suna shawagi a cikin ambaliyar ruwa, musamman a Bayelsa.

“Ya kamata gwamnati ta samar musu da sansani mai kyau da bandaki da ruwa da kuma kiwon lafiya domin za su bukaci a kai su asibiti domin kula da lafiyarsu,” inji Ojinmah.

 Bugu da kari, shugaban kungiyar likitocin Najeriya, Dr Emeka Orji ya bayyana cewa duk sanda aka samu ambaliya ta kan haifar da sakamako nan take da kuma nan gaba.

 "Ambaliya na iya haifar da cututtuka na ruwa kamar zawo, kwalara, da zazzabin typhoid.

 “Dole ne gwamnatocin jihohi da na tarayya su samar da matakan kariya don hana afkuwar wannan bala’i"

 Likitan ya kuma zargi sakacin gwamnatin me ya haddasa asarar da ambaliyar ta haifar.

"Yawancin lokaci, akwai gargaɗin cewa ambaliya za ta faru amma idan muna da isassun ƙungiyar ba da agajin gaggawa, da an hana hakan. Don haka ina zargin gwamnatin jiha da ta tarayya”.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci