OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Mutum 1 Ya Mutu, 18 Sun sun Jikkata A Arangama Tsakanin Magoya APC Da PDP A Zamfara

Mutum 1 Ya Mutu, 18 Sun sun Jikkata A Arangama Tsakanin Mago

Rundunar yan sanda a jihar Zamfara a ranar Lahadi ta tabbatar da mutuwar mutum daya, tare da jikkatar wasu 18 a wata arangama da wasu yan bangar siyasa suka yi.

 

Rundunar yan sandan ta ce ana zargin magoya bayan 'yan jam'iyyar APC da PDP ne na jihar suka aikata wannan aika aika.

 

Kakakin rundunar yan sanda na jihar Muhammad Shehu ne ya tabbatar da hakan a wani sakon kar-ta-kwana da ya aikewa kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Gusau ranar Lahadi.

 

Shehu, wanda ya tabbatar da cewa rundunar ta samu rahoton an kashe wani ya ce: "An fara bincike mai zurfi kan lamarin don tabbatar da cewa wadanda suka aikata laifin sun fuskanci hukunci

Sai dai kakakin ya ki yadda ya yi karin haske game da faruwar lamarin.

 

Wannan batu ya biyo bayan zargin da jamiyyar APC ta yi na cewa wasu yan banga da ake zargin PDP ne suka yi hayar su sun kai hari inda suka kashe mutum daya tare da raunata wasu 18 ba tare da sun yi musu wani laifi ba.

 

Zargin na APC na kunshe ne a wata sanarwa da Yusuf Idris, sakataren yada labaran jamiyyar a Gusau ya fitar ranar Asabar.

 

Mista Idris ya ce: 'abin takaici ne kuma abin damuwa ne game da harin da 'yan bangar jam'iyyar PDP suka kai.

 

Yan barandan sun zo ne a a matsayin 'yan bangan Gwamnan Jihar Zamfara a karkashin Jamiyyar PDP, inda suka harbe matasa da ba su ji ba ba su gani ba, wadanda ke aikin tsaftar muhalli na wata-wata a unguwar GRA da ke Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.

 

Ya ce an kai wa wadannan mutane hari ne saboda kasancewar su magoya bayan jam'iyyar APC ne.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci