OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Mutane 4 Sun Mutu Sanadin NitsewarJirgin Ruwa a Legas

Mutane 4 Sun Mutu Sanadin NitsewarJirgin Ruwa a Legas

Boat Mishap

Wani hatsari da ya afku a Legas yayin da wani kwale-kwale ya kife yayi sanadin mutuwar fasinjoji huɗu.

An ce wadanda lamarin ya rutsa da su har yanzu ba a san ko su waye ne ba, amma an tabbatar uku daga cikinsu ƴan gida ɗaya ne.

Ƴan majalisar dokokin jihar Legas ne suka tabbatar da hakan a ranar Litinin da ta gabata yayin da suke jajantawa iyalan waɗanda suka rasa ƴan uwansu a wannan hatsarin.

Da yake gabatar da jawabi, wakilin mazaɓar Kosofe II, Femi Saheed, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.

A cewar Saheed, “Mutane huɗu ne suka rasa rayukansu inda uku daga cikin wadanda suka mutu ƴan gida ɗaya ne, Abin takaici ne matuƙa da ba ma fatan ganin irinshi." 

A halin da ake ciki kuma, hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Ogun, TRACE, a jiya, ta bayyana cewa mutane biyu sun mutu yayin da wasu huɗu suka samu raunuka a wani hatsarin mota.

Hatsarin ya haɗa da wata motar bas, tirela da babur a kusa da Conoil Bus-Stop a kan babbar hanyar Legas zuwa Abeokuta, cewar Jaridar Vanguard.

Misis Temitope Oseni, Kwamandan sashin Owode-Ijako na TRACE, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin, ta bayyana a Ota cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:03 na rana.  ran Litinin.

Oseni ya bayyana cewa wata babbar mota kirar Daf blue mai lamba, AAA 094 XT, tana kan hanyar zuwa Abeokuta daga Sango-Ota a cikin sauri, kuma ta ci karo da wata mota kirar Mazda mai lamba FKJ 509 XX da kuma babur Bajaj.

Ta ce mutane shida ne hatsarin ya rutsa dasu inda mutane biyu suka mutu, yayin da wasu huɗu suka samu raunuka daban-daban.

“An kai gawarwakin waɗanda abin ya shafa asibitin ƙwararru ta jihar dake Ota, yayin da waɗanda suka tsira ke karɓar magani a asibiti.”

Oseni ya shawarci masu ababen hawa da su guji gudu da kuma tukin mota na ganganci don gujewa asarar rayuka da dukiyoyi.

Ta kuma shawarce su da su tabbatar da cewa motocinsu suna cikin yanayi mai kyau kafin a sanya su a kan tituna domin gujewa afkuwar hatsari.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci