OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Gwamnatin Legas tana biyan ma'aikata alawus din N35,000

Gwamnatin Legas tana biyan ma'aikata alawus din N35,000

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana tun a watan Janairu ma’aikatan gwamnatin jihar ke cin gajiyar na ci gaba da alawus N35,000 a kan albashin su.

 

Sanwo-Olu ya bayyana hakan a wani taron a jihar a ranar Alhamis. 

 

A cewarsa, nan ba da jimawa ba gwamnatin jihar za ta fitar da wani sabon tsarin mafi karancin albashi.

 

Gwamnan ya bayyana cewa wadanda a baya suke karbar mafi karancin albashi N35,000 tun daga farkon shekarar nan albashinsu ya koma N70,000.

 

"mun bayyana wannan kari a fili domin mutane su san cewa wannan gwamnati ta ninka adadin albashin ma'aikata don tabbatar da cewa a wannan mawuyacin lokaci, ba ta bar 'yan kasa cikin mawuyacin hali ba," in ji shi.

 

Tun bayan janye tallafin man fetur Al'ummar kasar ne ke kokawa bisa tsananin tsadar kayyakin masarufi da hauhawar farashin man fetur.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci