OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Miliyoyin kaddarori sun lalace yayin Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafe kauyen Jigawa

Miliyoyin kaddarori sun lalace yayin Da Ambaliyar Ruwa Ta Sh

Biyo bayan mamakon ruwan sama da aka yi a jihar Jigawa, ambaliyar ruwa a Gamayin ta lalata gidaje, gonaki da dukiyoyi na miliyoyi.

Rahotanni sun bayyana cewa, ambaliyar ruwar ta mamaye wata kauye a karamar hukumar Kafin Hausa.

Wani Malam Ibrahim Musa Gamayin da ke magana da yawun al’ummar ya ce gidaje da dama sun ruguje yayin da ambaliyar ta tilasta wa mazauna garin gudu domin tsira.

Ya kuma kara da cewa, ba a samu asarar rai sakamakon wannan iftila'in ba, amma gonaki da dukiyoyin miliyoyi na mutane sun salwanta.

A halin da ake ciki mataimakin gwamnan jihar Alhaji Umar Namadi ya bayyana bakin cikin sa kan lamarin.

Ya jajanta wa wadanda abin ya shafa tare da ba su tabbacin tallafi daga gwamnati.

Idan ba a manta ba, AllNews ta ruwaito mataimakin gwamnan ya bayyana cewa biyo bayan ambaliyar ruwa a jihar, akalla mutane 134 ne suka mutu yayin da sama da naira tiriliyan 1.5 suka salwanta.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci