OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Mutane biyar sun mutu sanadiyyar ambaliyar ruwa a jihar Delta

Mutane biyar sun mutu sanadiyyar ambaliyar ruwa a jihar Delt

Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta ya jajanta wa iyalan wadanda ambaliyar ruwa ya rutsa da su da kuma wadanda suka yi asarar dukiyoyi sakamakon ambaliyar.

 

Ya kuma kara da cewa gwamnatin jihar ta kafa sansanoni 11 don kula da wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.

 

Sannan gwamnan ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gina sabbin madatsun ruwa tare da yashe manyan koguna a kasar nan domin hana ambaliyar ruwa.

 

Mista Okowa, wanda ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ya ziyarci wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a wasu sansanonin yan gudun hijira, inda ya bayyana cewa mutane biyar ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa a jihar.

 

Ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta yi kokarin kara zurfin kogin Neja da Binuwai don ya iya daukar ruwan sama mai yawa.

 

Ya ce hanya mafi dacewa da za a kawo karshen asarar rayuka da dukiyoyin sakamkon ambaliyar ruwa ita ce gwamnati ta dauki matakan da suka dace don dakile ambaliyar ruwa a duk lokacin da kasashe makwabta suka bude madatsun ruwan su.

 

 

Ya ce ciyar da yan gudun hijirar a kullum abu ne da ya sa a gaba, kuma an aika da maaikata kiwon lafiya zuwa sansanoni daban-daban don kula da lafiyar 'yan gudun hijira domin gujewa barkewar cututtuka.

 

Premium Times Ta ruwaito

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci