OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Majalisar Wakilai Ta Nuna Ɓacin Rai Kan Jinkirin Kammala Aikin Titin Abuja-Kaduna-Kano 

Majalisar Wakilai Ta Nuna Ɓacin Rai Kan Jinkirin Kammala Ai

Majalisar wakilai ta bukaci ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, da ya umurci kamfanin Julius Berger Plc da ya gaggauta kammala aikin gyaran hanyar Abuja-Kaduna-Kano.

Kiran na zuwa ne bayan ƙudirin da Garba Datti Muhammad da wasu mutane 38 suka ɗauki nauyi a kan al’amuran da suka shafi muhimmancin jama’a a jiya.

Idan ba'a manta ba majalisar a cikin Maris 2021, ta canza farashin da ake yi na aikin na farko daga Naira biliyan 155 zuwa Naira biliyan 797.2.

A wancan lokacin, ministan ya shaida wa manema labarai cewa, “Takardar ta shafi babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Zariya zuwa Kano, domin sauya fasalin aikin gyaran fom din da aka bayar a baya.

"Saboda da dama daga cikin ɓangaren hanyoyin sun lalace, don sake gina tituna biyu, ta bangarorin biyu.” cewar Jaridar Daily Trust.

Majalisar ta ce biyo bayan yawaitar hare-haren ƴan fashi da makami a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, ɗan kwangilar ya janye ma’aikatansa saboda dalilai na tsaro.

“A lokacin da ɗan kwangilar ya janye, akalla rabin titin ne aka kammala, kuma an rufe shi ne daga baya wanda bayan tsananin ruwan sama da aka yi a watannin baya.

"Saboda yanayin hanyar a halin yanzu, abu ƙalilan ke jawo cunkoson abun hawa na awowi" in ji su.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci