OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Gwamnatin Tarayya na kokarin rage adadin mace-macen mata yayin haihuwa

Gwamnatin Tarayya na kokarin rage adadin mace-macen mata yay

A wani yunkuri na yaki da mace-macen mata masu juna biyu yayin haihuwa da inganta rayuwar jarirai, gwamnatin tarayya ta amince da ware Naira biliyan 25 ga cibiyoyin lafiya 8,800 a fadin kasar nan.

 

 Ministan lafiya Farfesa Muhammad Ali Pate, ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a Abuja don bikin ranar iyaye mata ta 2024 mai taken “Inganta lafiyar mata masu juna biyu don samun makoma mai dorewa". 

 

Farfesa Pate ya jaddada mahimmancin cikakkiyar kulawa da ta ƙunshi kafin haihuwa, yayin haihuwa, kulawa bayan haihuwa, da kuma tsarin iyali.

 

Ya yi kira ga masu ruwa da tsaki, malaman addini, da kafafen yada labarai, su bawa gwamnatin hadin kai domin tabbatar da samar da ingantaccen kiwon lafiya ga mata masu juna biyu.

 

 "Dole ne mu tabbatar da cewa dukkan mata a Najeriya sun samu ingantacciyar kulawar yayin haihuwa ba tare da an nuna musu wata wariyaba" in ji Farfesa Pate, yana mai jaddada gwamnati a shirye take ta tabbatar da ingancin kiwon lafiya ga alumma baki daya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci