OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Ministan ma'adanai ya soke lasisin kamafanoni 924

Ministan ma'adanai ya soke lasisin kamafanoni 924

Minister of Solid Minerals Development, Dr Oladele Alake

Ministan ma’adanai na kasa, Dakta Dele Alake, ya amince da soke lasisin kamafanonin hakar ma’adinan 924 da suka dade basa aiki da shi.

 

 Ministan ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedkwatar ma’aikatar da ke Abuja. 

 

Yace dalilin da yasa aka soke lasisin shi ne ganowa da aka yi akasarin masu lasisin hakar ma’adinan suna amfani da su wajen yiwa fannin hakar ma'adanai zagon kasa.

 

 Allnews.ng ta tattaro cewa a watan Janairun daya gabata ministan ya sanar da cewa za a cigaba da kara janye lasisin hakar ma'adanan a shekarar 2024 a kokarin da ake na sake farfado da fannin hakar ma’adinai ya Zama hanyar samun kudin shiga a kasarnan.

 

Dele Alake ya kuma ce manufar ma'aikatar sa a wannan shekarar shine samar da sauye-sauyen da zasu bunkasa fannin hakar ma'adanai a kasarnan.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci