OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Barazanar Ta'addanci: Buhari Zai Yi Ganawar Gaggawa Da Shugabannin Tsaro 

Barazanar Ta'addanci: Buhari Zai Yi Ganawar Gaggawa Da Shuga

A yau Litinin ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gana da shugabannin tsaro a birnin tarayya Abuja, domin ci gaba da nazari da kuma karfafa harkar tsaro a kasar.

 Hakan ya fito ne a daren jiya ta wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Mallam Garba Shehu ya fitar.

 Sanarwar ta bayyana cewa, shugaban wanda aka shirya tun da farko zai kaddamar da sabuwar cibiyar fasahar kere-kere ta kasa (NASENI), zai karbi bayanai daga shugabannin jami’an tsaro, domin yin nazari kan wuraren da ke bukatar karin kulawa.

 Sanadin hakan aka ɗage kaddamar da aikin na NASENI zuwa nan gaba.

 A baya, an samu sanarwar tsaro cewa 'yan ta'adda sun shirya kai hari a wasu wuraren da aka ware a Abuja, babban birnin kasar nan.

 Hakan dai ya haifar da firgici a Abuja kuma a kwanakin baya kasashen Birtaniya da Amurka a shawarwarin tsaro na daban sun shawarci ‘yan kasar su barin Abuja.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci