OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Fittacen jarumin Nollywood Zulu Adigwe ya rasu

Fittacen jarumin Nollywood Zulu Adigwe ya rasu

Zulu Adigwe

Jarumin a masana'antar shirya fina-finai Nollywood na cigaba da alhinin  rasuwar fitaccen jarumi, Zulu Adigwe.

 

An sanar da mutuwar Adigwe da yammacin jiya Talata

Mai shirya fina-finai a masana'antar Stanley Nwoko ne ya sanar da rasuwar jarumin a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram.

 Sakon ya tabbatar da har yanzu ba gane musabbabin mutuwar Adigwe ba.

 

Nwoko ya wallafa “ina nadamar sanar muku da rasuwar wani fitaccen dan wasan kwaikwayo, marigayi Mista Zulu Adigwe". 

 

Adigwe ya fito a shahararrun fina-finai a masana'antar kamar su Breaking Free", da dai sauransu. 

 

Idan zaku iya tunawa masana'antar fina-finai ta Nollywood ta yi rashin jaruman ta shida a shekarar 2024.

 

Wadanda suka hada da; Sisi Quadri, Mista Ibu, Amaechi Muonagor, Andy Best, Jumoke Aderounmu da kuma Junior Pope.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci