OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Kotu ta kori karar da EFCC ta shigar akan Adoke

Kotu ta kori karar da EFCC ta shigar akan Adoke

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja a ranar Juma’a, ta wanke tsohon ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF), Mohammed Bello Adoke daga tuhume-tuhumen da ake yi masa na halasta kudaden haram da almundahana da aikata laifukan cin hanci da rashawa.

Alkalin kotun, Mai shari’a Inyang Ekwo ya yi watsi da karar ta biyu da EFCC ta shigar a kansa.

A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Ekwo, ya ce EFCC ba ta bayar da wata shaida da za ta tabbatar da muhimman abubuwan da suka shafi laifin da ake tuhumar Adoke dasu ba.

 

Hukumar EFCC ta gurfanar da Adoke da wani dan kasuwa mai suna Abubakar Aliyu, a gaban kotu a shekarar 2017 kan zargin karkatar da kudade har Naira miliyan 300.

 

Hukumar ta kuma tuhumi ministan da rubuta haramtacciyar yarjejeniya a sa'ilin sayar da wani OPL 245 a gaban mai shari'a Abubakar Kutigi

A cikin jawabin da ta gabatar a gaban mai shari’a Ekwo, EFCC ta ce Adoke ya aikata laifin ne a lokacin da ya karbi jinginar gida daga bankin Unity, inda hukumar tace kudin na cin hanci ne daga siyar da wani rukunin OPS da kamfanin Malabu Oil & Gas Ltd ya yi a shekarar 2011.

A zaman da aka yi tun farko a ranar 28 ga watan Maris, Mai shari’a Kutigi, yayi yake watsi da tuhumar da ake yi wa Adoke da sauran wadanda ake tuhuma sanadiyar sabanin da ke cikin bayanan Hukumar EFCC.

Kutigi ya kuma caccaki hukumar yaki da cin hanci da rashawa da rashin gudanar da bincikenta da kyau da kuma bata wa kotu lokaci na tsawon shekaru hudu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci