Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabi'u Kwankwaso, ya bayyana cewa wasu kadarorinsa ya ke siyarwa domin cigaba da tallafawa karatu dalibai a jami'a.
Inda ya yi alkawarin ci gaba da yin kokari wajen ganin Najeriya ta samu ci gaba.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a wajen taro karo na 3 wanda kungiyar Kwankwasiyya Development Foundation ta shirya domin bikin cikarsa shekaru 66 a ranar Litinin a Abuja.
Tsohon gwamnan jihar Kano ya bayyana ilimi a matsayin jarin ‘yan siyasa da za su sakawa al’umma, inda ya ce ya taba saka hannun jari a fannin ilimi da ci gaban dan Adam saboda tasirin da suke da shi a rayuwar jama’a.
Sanata Kwankwaso, wanda ya ce a koda yaushe ya na ba wa kansa abin da zai yi wa mutane, ya ce sama da dalibai 3,000 ne suka ci gajiyar shirin tallafin karatu a shekarar 2011 zuwa 2015 lokacin da ya ke gwamnan jihar.
0 Tsokaci