OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

2023: Ziyarar Atiku Zuwa Neja da Edo Alamar Nasara Ce - Ologbondiya

2023: Ziyarar Atiku Zuwa Neja da Edo Alamar Nasara Ce - Olog

Kungiyar yakin neman zaben Atiku/Okowa na jam’iyyar PDP ta bayyana cewa ziyarar da Atiku ya kai jihohin Edo da Neja alama ce ta samun nasara.

Kungiyar yakin neman zaben ta yi wannan tsokaci ne biyo bayan dimbin jama’ar da suka tarbi dan takarar shugaban kasan a tarukan daban-daban.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar, Kola Ologbondiya ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa sanarwar ta bayyana cewa, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, Atiku Abubakar ya samu tarba daga dimbin jama'a a jihohin Benin, Neja da Katsina.

Ologbondiya ya ce tarbar ta nuna cewa jam’iyyar za ta lashe zaben shugaban kasa a 2023.

Da yake bayyana dalilin da ya sa yakin neman zaben ke kara samun karbuwa a fadin kasar, ya ce hakan ya biyo bayan "Aniyar sa (Atiku) na farfado da tattalin arzikin kasar tare da sanya hadin kan al’ummar mu a matsayi tsintsiya madaurin ki daya, da zaman lafiya a tsakanin ‘yan Najeriya."

Ya kuma kara jaddada aniyar dan takarar shugaban kasa na yaki da matsalar rashin tsaro a kasar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci